An sami Abu Walaa da alaka da IS
February 24, 2021Talla
Wata kotu da ke birnin Celle a arewacin Jamus ta sami Abdulaziz Abdullah wanda aka fi sani Abu Walaa da laifin zama mamba da kuma tallafawa kungiyar IS.
Limamin masallacin da tuni aka zargi masallatan da tsatsauran ra'ayi, ya kasance wakilin kungiyar ta IS a kasar wanda kuma ya ke yaudarar matasa tare da sakasu cikin kungiyar.
Bayan kotun ta same shi da laifi ta kuma yanke masa hukuncin shekaru goma da rabi a gidan kasu.