An sami bullar cutar Ebola a Kongo
May 9, 2018Talla
Wannan na zuwa ne bayan da jami'an kiwon lafiya a yankin suka soma baiyana fargaba kan wasu mutane ashirin da biyu da suka nuna alamun cutar, akwai wasu goma sha bakwai da suka riga suka mutu da ake zaton a sanadiyar cutar ce.Tuni aka dauki matakin dakile cutar. Yanzu haka ma dai an tura kwararru yankin don sa ido da kuma hana bazuwar cutar da ke saurin halaka dan adam. Rahotannin na cewa wannan shi ne karo na tara da cutar ta Ebola ke bulla a jamhuriyar Kongon.