An sami sauki a hukuncin kisa
April 11, 2017Talla
Wani sabon rahoton da kungiyar ta Amnesty International ta fitar, na nunin cewa an sami raguwa kan hukuncin kisa a Amirka da ma sauran kasashen duniya. Yanzu dai a cewar rahoton Amirkar ta fita daga jerin kasashe 5 da suka fi yawan daukar matakin kisa kan jama'a.
Haka ma batun yake a kasashen Iran da Pakistan da ke yawan gudanar da hukuncin. Akwai ma wasu kasashen Afirka kudu da hamadar sahara da suma rahoton ya ce an sami wannan sauki.
Amnesty ta ce mutane dubu daya da talatin da biyu aka yankewa hukuncin kisa a duniya, abin da ke zama wani sauki na kashi 37 cikin dari cikin shekaru biyu da suka gabata.