An samu asarar rayuka a Chadi
April 27, 2021Masu zanga-zangar sun karade titunan birnin inda suke ambaton lafazin "Wakit Tama" wato lokaci ya yi. Da sanyin safiyar yau Talata ce aka jiyo hayaniyar dubban matasa a kan titunan suna nuna kin amincewa da matakin da majalisar sojojin kasar ta dauka wanda kuma ke samun goyon bayan Faransa na nadin Muhammat Idris Deby a matsayin shugaban kasar sa'oi kalilan bayan rasuwar mahaifinsa.
Yan adawa da kungiyoyi masu zaman kansu ne suka kira jerin gwanon da ya haddasa asarar rayukan mutane biyu. Tun dai da yammacin jiya ne mahukuntan Chadin suka haramta zanga-zangar.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi Allah wadai da tashin hankalin da zanga-zangar ta haddasa yayin da yake karbar bakuncin shugaban jamhuriyar Damakaradiyar Congo kuma shugaban kungiyar tarayyar Afirka Felix Tshisekedi.