1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaNa duniya

WHO: Bullar sabon nau'in corona

August 18, 2023

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da hukumomin Amurka sun sanar da gano wani sabon nau'in kwayar cutar COVID-19, inda suka ce suna sa ido a kansa duk da ba su kai ga tantance girman tasirinsa ba.

Duniya | Annoba | Corona | COVID-19
Bullar sabuwar kwayar cutar corona ko COVID-19Hoto: DW

Hukumomi biyu sun ce sun yanke shawarar gudanar da bincike domin rabe bambance-bambancen da ke akwai tsakanin sabon nau'in kwayar cutar da suka yi wa lakabi da BA.2.86 da wancan na baya, la'akari da adadi mai yawa na kwayoyi masu saurin ninkawa da ya kunsa wadanda yawansu ya haura maki 30. Da ma dai a wani rohoto da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fitar a baya-bayan nan, ta ce a tsukin 17 ga watan Yuli zuwa 13 ga watan Agusta na wannan shekarar an samu mutane miliyan guda da dubu 400 da suka kamu da cutar COVID-19. Cikin wannan adadi dai, mutane dubu biyu da 300 suka bakunci lahira. Adadin na nuni da cewa tun bayan lafawar annobar, an samu karuwar masu kamuwa da ita da kaso 63 cikin 100.