1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu karin sayen makamai a 2017

Kersten Knipp ATB
May 2, 2018

A rahoton da ta fitar cibiyar binciken zaman lafiya ta kasa da kasa da ke a Stockholm ta ce an sami karin kashe kudade wajen sayen makaman soji a duniya a shekarar 2017 idan aka kwatanta da yadda lamarin yake a 2016.

China Peking Militärparade
Hoto: picture-alliance/ANN

A bisa alkaluman da cibiyar binciken zaman lafiyar ta duniya ta fitar, ta ce ko da yake karin kudaden da aka kashe wajen sayen makamai a duniya baki daya a 2017 ba masu yawa ba ne amma idan aka kwatanta da shekarar 2016 adadin ya kai dala biliyan 1,739 kwatankwacin karin kashi 1.1 daya na kiyasin abin da aka kashe a 2016.

A wata hira da tashar DW shugaban cibiyar binciken zaman lafiyar ta duniya SIPRI da ke Stockholm Pieter Wezeman ya ce karin kashe kudaden kan makamai ya banbanta daga yanki zuwa yanki da a tsakanin kasashe. Alal misali kasar China a yanzu nesa ba kusa ba ita ce ta biyu a duniya wajen kashe kudi kan makamai baya ga kasar Amirka. Kuma kasancewar ta kasa mai karfin tattalin arziki a yankin Asia tana so ta ga ta karfafa tasirinta ta fuskar karfin soji a yankin da ma duniya baki daya.

Ita ma dai kasar Amirka ta kara yawan kudaden da take kashewa akan makamai duk da alkawarin da Trump ya yi na rage kashe kudin akan makamai. Sai dai a cewar Pieter Wezeman yana ganin Trump yana da kudirin kara kudi kan sayen makamai: "Ni a gani na Donald Trump yana so ya kara yawan kashe kudade kan makaman soji kuma ya kudiri kara yawan kasafin kudi ga wannan bangare a kasafin 2018, sai dai ko zai kasance kari ne mai yawa ko kuma akasin haka kamar yadda gwamnatin ta Trump take nunawa lokaci ne zai tabbatar da hakan."

Saudiyya ta shiga yaki a kasashen yankintaHoto: picture-alliance/dpa/K. El Fiqi

Kashe kudaden akan sayen makamai ya fi kamari ne musamman a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, inda kasashe bakwai daga cikin kasashe goma suka kebe makudan kudade akan haka. Wadannan kasashe sun hada da Oman da Saudiyya da Kuwait da Jordan da kasar hadaddiyar daular Larabawa da Katar da Isra'ila da Lebanon wadanda suka ware fiye da kashi goma cikin dari na abin da suke samu a shekara wajen sayen makamai.

Kasar Saudiyya na kashe kudi mai yawa bisa gogayya da abokiyar hamaiyarta Iran da kuma yakin da ta ke yi a Siriya da Yemen. A nata bangaren Iran tana son kara kudade kan makamai amma matsalolin tattalin arziki da ta ke fuskanta ba za su bar ta ta yi hakan ba. Kasashen tsakiyar Turai a nasu bangaren sun kara yawan abin da suke kashewa kan makamai da kashi 12 cikin dari yayin da kasashen Yammacin Turai suka kara da kashi 1.7 cikin dari lamarin da mai yiwuwa baya rasa nasaba da barazanar da suke fuskanta daga Rasha.

Yaki da 'yan ta'adda na neman zama ruwan dareHoto: picture-alliance/dpa/Imaginechina

A nan Jamus ma dai ministar tsaron kasar Ursula Von der Leyen ta yi tsokaci kan karin kudaden makaman gabanin gabatar da kasafin kudin shekarun 2018 da 2019 inda take cewa: "Yana da muhimmanci a samar da kudi mai tsoka ga lamarin tsaro a shekaru masu zuwa. Wannan batu ne mai muhimmi don yaki da ta'addanci da samar da kwanciyar hankali a kasashe makwabtan Turai inda kawancen hadin gwiwa ke da matukar tasiri ga aikin kiyaye zaman lafiya da sojojin Jamus ke yi".

Ita ma dai kungiyar tsaro ta NATO ta kara yawan kudaden da take kashewa akan makamai, sai dai kuma Rasha a waje guda ta rage abin da take kashewa kan makaman idan aka kwatanta da shekarun 2016 da 2017 da suka gabata.