Rikicin kabilancin Sudan ya halaka mutane 130
January 18, 2021An samu karin alkaluman mutanen da suka halaka sakamakon rikicin tsakanin Larabawa da sauran kabilun Lardin Darfur na yamamcin Sudan zuwa mutane 130, yayin da wasu kusan 200 suka jikata, da suka hada da mata da yara, a cewa likitoci da ma'aikatan jinya. A daren Lahadi fadan ya ta'azzara tsakanin kabilun da suka dade suna samun sabani da juna.
Tun farko Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna takaicin kisan yankin Darfur yayin da gwamnan lardin ya kada dokar hana fitar dare bayan tashin hankalin na kabilanci. Rikicin ya ta'azzara makonnin biyu bayan kawo karshen aikin dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke shirin janyewa daga yankin baki daya, inda fiye da mutane 50,000 suka rasa matsugunai sakamakon sabon rikicin.
Tun daga shekara ta 2003 kimanin mutane 300,000 suka halaka. Ana zargin kunyoyin masu dauke da makamai suna amfani da janye dakarun kiyaye zaman lafiya domin tayar da hargitsi a yankin na Daruife da ke Sudan.