Karuwar aikata laifukan kisa a kasar Ecuador
August 21, 2025
Wata kididdiga da ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Ecuador ta fitar a wannan Alhamis ya nuna cewa an samu karuwar kashe mutane a kasar da kaso 40 cikin 100 a watanni bakwai na farkon wannan shekara ta 2025, inda aka kwatanta da watanni bakwai na farkon shekarar da ta gabata ta 2024. Kimanin mutane 5,268 aka halaka cikin yanayi na aikata laifuka a kasar da ke yankin kudancin Latin Amurka a wannan shekara ta 2025.
Karin Bayani: Fursononin Ecuador sun yi garkuwa da gandurobobi
Galibin mutanen da aka halaka sun kasnace 'yan shekara 25 zuwa 34 a cewar rahoton na hukumomi. Wannan duk da matakan da Shugaba Daniel Noboa na kasra ta Ecuador ke dauka domin yaki da miyagun laifuka a kasar. Ita dai gwamnatin kasar ta daura alhakin abin da ke faruwa kan kan rikice-rikice tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai na kasar.