An samu koma baya a jarrabawar dalibai a Kamaru
July 23, 2024Dalibai dubu 133 da 868 ne suka yi rajistar shiga jarabawa bana, daga cikin su akwai mutum dubu dari da 32 132,920 suka gabatar da kansu a jarrabawar, yayin da 848 suka kaurace. An kuma samu dalibai 11 da laifin satar amsa. Jimillar dalibai dubu 36 da 615 sun yi nasarar samun jarrabawa wanda ya kai kaso 27.6 a duk fadin kasar ta Kamaru.
Jarrabawar Baccalaureats ta 2024 dai ta samu matsala ta satar amsa inda wasu dalibai suka dinga sayan amsa a shafukan sada zumunta, lamarin da ya kai ga ministar ilimin sakandare a Kamaru, Poline Nalova Lyonga nuna bacin rai inda ta ce, sune ke da laifi, domin ba a dauki mataki na shawo kan matsalar ba. A cewarta daga shekara mai zuwa za su dauki matakan da suka dace wajen shawo kan matsalar, inda za a rarraba wa dalibai takardun jarrabawar nan take kafin a fara rubutawa.
Baya ga laifin iyayen wajen kula da yaransu su kansu daliban nada nasu laifi domin ba su maida hankali a karatu ba, sun fi maida hankali ne a intanet musamman ma kafafen sada zumunta kamar yadda Malamar jami'a ta ce
Yawancin lokuta idan aka samu matsala, akan dora wa iyayen yara laifi ko su kansu yaran, duk da cewa gwamnati ita ce ke sahun gaba wajen kula da ilimin yara ko daukar matakan da suka dace wajen magance matsalolin da ake samu musamman ma lokutan jarrabawa a kasar Kamaru.
Yankin arewa maso yamma a sashen renon Inglishi, shi ne na farko a cikin yankuna goma da aka fi samun nasara da kaso 46.09%, wanda ya yi kasa idan aka kwatanta da 2023 kaso 84.08%. A matsayi na biyu kuma shi ne Littoral da 45.98%, shi ma ya ragu idan aka kwatanta da bara da kaso 78.47%. Sai kuma yankin yammaci da kaso 44.75% a bana, yayin da a bara ya samu kaso 80.34%.