1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu sabanin ra'ayi kan harin Amirka a Siriya

Yusuf Bala Nayaya
April 7, 2017

kasashen duniya sun bayyana ra'ayoyinsu dangane da harin da Amirka ta kaddamar kan sansanin sojan saman Siriya. Faransa da Jamus na daga cikin kasashen da suka yaba wannan mataki, yayin da Rasha da Iran suka yi suka.

Syrien USA Luftangriff auf Militärbasis
Hoto: Reuters/U.S. Navy/F. Williams

 

Za a iya cewa baki ya kusan daya kan matakin na Amirka tsakanin kasashe da suka mai da martani baya ga Iran da Rasha da suka yi tofin Allah tsine. Rashar dai ta mayar da martani mai kaushi ga mahukuntan na Amirka kan wannan hari inda kasar ta ce ta ajiye duk wata hulda da Amirka a kokari na warware rikicin Siriya.

A cewar Sergei Lavrov ministan harkokin wajen Rasha babu wani dan Rasha da aka kashe a harin da ya halaka mutane bakwai a cewar Siriya inda mahukuntan ta Moscow ke bukatar dalili kan aikatashi, ganin ba a kai ga kammala bincike ba kan wanda ya kai harin mai guba. A cewar Maria Zakharova,mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rasha dama harin na wannan Juma'a an shiryashi tun kafin ma hari da aka samu an kai a ranar Talata.

Shugaba Putin na Rasha bai ji dadin harin da Amirka ta kai Siriya baHoto: picture-alliance/dpa/M. Metzel

Ta ce " afayyace yake cewa mahukuntan Washington sun shirya harin na makami mai linzami kafin abin da ya faru a Idlib ranar Talata, abin da aka yi amfani da shi domin gwada karfin soja."

A cewar gwamnan birnin Homs Talal Barazi ruwan makamai masu linzami da Amirka ta kaddamar a sansanin sojan Siriya na Shayrat ya yi sanadi na rayukan mutane baya ga jirage na soji da aka lalata.

Jamus da Faransa sun yi na'am da harin Amirka a Siriya

Faransa  da Jamus sun kalli wannan mataki na Amirka a matsayin hanya da za ta bude samar da sauyi a Siriya bisa jagoranci na MDD. Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel  ya ce matakin na Amirka dai na kan hanya.

Ya ce "abu da ke da muhimmanci shi ne sabanin kwanakin baya Amirka ta tashi daga batun cewa Shugaba Assad ya ci gaba da zama a kan kujerar mulki, mu karkata kan yaki da ta'addanci, wannan shi ne abin da ya damu kasashen Turai a murkusheshi."

Daga can ma Ostareliya da ke cikin kawance na Amirka Firaminista Malcolm Turnbull ya ce matakin na Amirka abu ne da zai taka wa mahukuntan kasar Siriya birki a kokari na amfani da makami mai guba nan gaba.  

Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel ya yi na'am da matakin AmirkaHoto: DW/B. Riegert

Ya ce "tasirin mayar da martanin da Amirka ta yi zai rage kaifin kokari na gwamnatin Siriya wajen kai hari da makami mai guba abin da ke kada zuciya a 'yan kwanakin nan, kuma Amirka ta sanar da kawancenmu gabannin kai wannan hari."

A Japan kuwa Firaminista Shinzo Abe ya ce matakin da gwamnatin Amirka ta dauka kokari na samar da zaman lafiya a duniya.

Ya ce "mahukuntan Tokyo sun yi nazari kan matakin na Shugaba Trump kuma wannan ke kokari na nuna neman kasashen duniya su zamo masu bin doka da oda abin da zai samar da zaman lafiya da tsaro a kasashe kawayen Amirka a duniya."

Italiya ma dai na da irin wannan ra'ayi, da ke zuwa a daidai lokacin da kwarrarrun masana kan ce da shakku kan hakikanin wanda ke da hannu a harba makami mai gubar bangaren gwamnatin Assad ne ko na 'yan tawaye. Tuni dai Shugaban Faransa Francois Hollande  ya kira wani taro na gaggawa kan matakin da za a dauka na gaba kan rikicin na Siriya bayan da aka kai ga wannan gaba.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani