1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSweden

An samu wani da ya kamu da cutar Kyandar Biri a Sweden

August 16, 2024

Wani dan asalin kasar Sweden ya kamu da kwayar cutar Kyandar Biri, cutar da ke kokarin zama wata babbar baraznar lafiya a duniya, a cewar hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya.

Hoto: Sven Hoppe/dpa/picture alliance

A karon farko, cutar kyandar biri ta bulla a wata kasa da ke wajen nahiyar Afirka, inda Sweden da ke cikin kasashen yankin Scandinavia ta sanar da kamuwar wani mutum guda a jiya Alhamis.

Hakan ya zo ne kwana guda bayan Hukumar Lafiya ta Duniyo WHO, ta bayyana kwayar cutar nau'in ''clade 1'' a matsayin wata barazana a fannin lafiyar duniya a yanzu.

A bara ne dai nau'in ya bulla a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, da kuma ta yadu zuwa ga kasashe makwabtanta daga bisani.

Ma'aikatar lafiya ta kasar Sweden din ta ce d'an kasar da cutar ta kama, ya nuna alamunta ne bayan ziyartar yankin Afirka da cutar ke ciki da ya yi a baya-bayan nan.

Kyandar birin dai cuta ce da fara kama bil Adama a shekarun 1970 a Kwango, bayan ta samo asali daga birrai.