Ministar harkokin kasashen wajen Ruwanda ta samu mukami
October 12, 2018Talla
Jim kadan bayan samun wannan matsayi Mushikiwabo ta jaddada aniyar ta ta ba harshen Faransanci fifiko saboda yadda yaren ya bazu a fadin Duniya,a baya dai kasar Ruwanda ta dora alhakin rikicin kabilancin da ya faru a kasar a shekara ta 1994 kan kasar Faransa lamarin da ya haddasa tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu. Tuni dai shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya taya sabuwar babbar magatakardar Kungiyar kasashe Rainon Faransan murna.