Masu zanga-zanga a sudan sun zargi sojoji da yaudara
April 15, 2019Wannan nadi na zuwa ne a daidai lokacin da masu shirya zanga-zangar dake gudana yanzu haka a kasar suka umarci magoya bayansu da su ci gaba da yada manufofin juyin juya hali ga sauran jama'ar da ke harabar shalkwatar sojojin kasar, bayan sun tabbatar da samun labarin shirin da sojojin na tarwatsa zaman dirshan din da kungiyoyin masana suke yi har na tsawon kwanaki 10 da nufin bayyana wa duniya takaicinsu game da karbe ragamar mulkin kasar ta Sudan da sojoji suka yi.
Tun da fari sabuwar gwamnatin rikon kwaryar karkashin jagorancin soji ta dauki alwashin samar da gwamnatin rikon kwarya ta farar hula tare da alkawarin mika mulki ga farar hula cikin kasa da shekaru biyu bayan wata tattaunawa da bangaren gwamnati mai barin gado da kuma tawagar 'yan adawar kasar, batun da a halin yanzu masu zanga-zangar suka ayyana a matsayin yaudara duk kuwa da cewar sun mika wa gwamnatin rikon kwaryar jadawalin bukatunsu jim kadan bayan hambarar da shugaba Omar al-Bashir wanda ya kwashe kimanin shekaru 30 yana mulki.