1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An sanya dokar hana zirga-zirga a Lamurde na jihar Adamawa

July 12, 2025

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar SP Suleiman Nguroje ya tabbatar wa da wakilinmu Mubarak Aliyu matakan da suke dauka domin dakile rikicin.

Gwamnan jihar Adamawa Umaru Fintiri
Gwamnan jihar Adamawa Umaru Fintiri Hoto: Abdulraheem Hassan/Domiya Terry/DW

Gwamnatin jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ta ayyana dokar ta baci ta hana zirga-zirgar mutane na tsawon sa'o'i 24 a karamar hukumar Lamurde da ke kudancin jihar, bayan samun rahotannin mutuwar kimanin mutane hudu a wani sabon rikici na kabilanci.

Kazalika kwamishin 'yan sandan jihar Dankombo Morris ya kaddamar da kwamitin bincike kan musabbabin afkuwar lamarin, tare kuma da jibge 'yan sandan kwantar da tarzoma a yankin na Lamurde domin tabbatar da doka da oda.

Karin bayani:ISWAP ta dauki alhakin halaka kiristoci a Arewacin Najeriya 

Ko a farkon wannan wata na Yuli da muke ci, an samu tashin hankali a kauyukan Lafiya da Boshikiri da ke kananan hukumomin Lamurde da Guyuk a jihar ta Adamawa.