An sanya hannu kan sabon shirin tsagaita wuta a Sudan ta Kudu
August 25, 2014Bangarorin da ke yakar juna a Sudan ta Kudu sun sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta inda suka sha alwashin kawo karshen rikicin da aka shafe watanni takwas ana yi. Masu shiga tsakani sun yi barazanar sanya musu takunkumai matukar yarjejeniyar ta sake rugujewa. Kungiyar kasashen gabashin Afirka ta IGAD wadda ta shiga tsakani a tattaunawar tsakanin Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar, ta yi kira ga shugabannin da su kafa gwamnatin hadin kan kasa a cikin kwanaki 45. Sanarwar bayan taron da aka yi a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ta yi maraba da yarjejeniyar wadda ta wajabta wa marikitan da su kawo karshen rikicin. Dubun dubatan mutane aka kashe sannan fiye da miliyan 1.8 suka tsere daga yakin basasan da ya samo asali daga gwagwarmayar rike madafun iko tsakanin Salva Kiir da Riek Machar, wadanda a wannan Litinin suka gana karon farko cikin sama da watanni biyu.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane