An sauke wasu jami'an gwamnatin Libiya
September 17, 2012 Ministan harakokin cikin gidan Libiya Fawzi Abdelali, ya sauke mukaddashin ministansa Wanis al Charef da shugaban hukumar tsaro ta kasa janar Hussein Bou Hamida. Wannan matakin ya biyo bayan harin da ya rutsa da jakadan kasar Amirka Chris Stevens da wasu jami'an ofishin jakadancin guda ukku a ran 12 ga watan nan. A cikin wata sanarwar da kanfanin dillanci labaran Faransa na AFP ya samu karantawa, ministan ya ce ya yi hakan ne domin kawo sauye-sauye a fannin tsaro na kasar.
Sanarwar ta ce an nada kanar Salahedine Dogman ya maye gurbin shugaban ma'aikatar tsaro ta kasar. Wannan na zuwa ne a dai-dai liokacin da kasashen musulmai a duniya ke zanga zangar nuna kyamar kasashen Yammaci, a dangane da wani mumunan fim din da ke walakanatar da manzon Allah Annabi Muhammadu.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Usman Shehu Usman