1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shari'ar tube rigar kariya ga Bazoum Mohamed

Gazali Abdou Tasawa SB
May 10, 2024

A Jamhuriyar Nijar babbar Kotun kasa ta Cour d'Etat ta dage zaman shari'ar neman tube rigar kariya ga hambararren shugaban kasa Bazoum Mohamed har ya zuwa watan Yunin gobe.

Bazoum Mohamed hambararren shugaban kasar Jamhuriyar Nijar
Bazoum Mohamed hambararren shugaban kasar Jamhuriyar NijarHoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Kotun ta dauki wannan mataki ne a yanzu, bayan da a zamanta na farko ta yi watsi da bukatar da lauyoyin Bazoum din suka shiga a gabanta na ganin ta dage zaman shari'ar  domin ba su damar sanin abin da takardun tuhumar suka kunsa ta yadda za su iya kare shi a gaban kuliya. Tuni dai kungiyar lauyoyin Nijar da ma wasu makusantan hambararren shugaban kasar suka fara bayyana matakin dage shari'ar da wata babbar nasara.

Karin Bayani: Nijar: Ina makomar Jam'iyyar PNDS Tarayya?

Magoya bayan Bazoum Mohamed hambararren shugaban kasar Jamhuriyar NijarHoto: AFP

Da misalin karfe 10 na safiyar wannan Juma'a ne 10 ga watan Mayun 2024, babbar kotun kasar ta Cour d'Etat mai kunshe da alkalai 23, ta bude zaman shari'ar a birnin Yamai. Sai dai lauyoyin hambararren shugaban kasar wadanda a zaman farko suka bukaci kotun da ta dage zaman da ba su damar gana wa da shi da ma ganin takardun tuhumar da ake yi masa ta yadda za su fi iya ba shi kariya, ba su halarci zaman shari'ar ba na yau. Amma kungiyar lauyoyin kasar ta halarci zaman domin kawo goyon baya ga lauyoyin Mohamed Bazoum game da bukatar. Kuma soma zaman shari'ar ke da wuya babban alkalin kotun ta Cour d'Etat ya sanar da karbar uzurin lauyoyin hambararren shugaban kasar tare da dage zaman shari'ar har ya zuwa ranar bakwai ga watan Yunin gobe.

Zaman kotun na yau ya wakana a gaban 'yan kallo. Sai dai babu ‘ya'yan jam'iyyarsa PNDS Tarayya ta hambararren shugaban da suka halarci zaman kotun. Illa wasu daga cikin ‘yan siyasa magoya bayan hambararren shugaban. Yanzu dai ‘yan kasa sun zura ido su ga zuwan ranar ta bakwai ga watan Yuni domin ganin yadda za ta kaya tsakanin alkalan kotun ta Cour d'Etat da lauyoyin hambararren shugaban kasar wanda hukumomin mulkin sojan kasar ke son a tube masa rigar kariya domin ba su damar gurfanar da shi a gaban kuliya kan jerin tuhume-tuhume da suke yi masa da suka hada da zargin cin amanar kasa.