1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniAfirka

An share fagen wasannin cin kofin nahiyar Afirka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim AMA
October 14, 2024

Aski ya zo gaban goshi a wasannin share fagen tunkarar gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2025 , bayan da aka shiga matakin gudun yada kanin wani.

'Yan wasan Najeriya da na Côte d'ivoire a gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2024
'Yan wasan Najeriya da na Côte d'ivoire a gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2024Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

A kokarin da kasashen Afirka ke yi na neman gurbi a gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a gudanar badi a kasar Maroko, an gudanar da wasannin share fage da dama a karshen mako. Amma Super Eagles ta Najeriya ta ce ba za ta buga wasanta da Libya na Talatar ba, sakamakon yadda hukumomin kasar suka bar 'yan wasan Najeriya a filin jirgi sama da sa'o'i 15 ba tare da abinci ko ruwa ba, in ji kyaftin dinta William Troost-Ekong.

Gasar firimiyar Najeriya ta shiga mako na shida

Ahmed Musa dan wasan Najeriya Hoto: Reuters/T. Hanai

Ana ci gaba da fafatawa a gasar firimiyar Najeriya da ta shiga mako na shida, kuma ta samu karin tagomashi bayan da kyaftin Super Eagles ta Najeriya Ahmad Musa tare da mai tsawon bayanta Shehu Abdullahi suka yi kome tsohuwar kungiyarsu ta Kano Pillars, daukacinsu nan ne mafarin samun alherinsu na haskakawa a duniya. Ko da ya ke Pillars din ba ta ji da dadi ba a hannun Akwa United bayan shan kashi da ci 2-0, wadda tsohon mai horaswarta Muhammad Baba Ganaru ke jagoranta, kuma yanzu haka ta na makale a mataki na 11 daga cikin kungiyoyi 20 na gasar.

Wasannin kasashen Turai wato Uefa Nations League na tafiya a tsanake 

Wasannin kasashen Turai na UEFA Nations League 2024Hoto: Andrzej Iwanczuk/NurPhoto/IMAGO

Daga fagen kwallon Tennis kuma Novak Djokovic ya gaza lashe kofi na 100 na gasar wasannin Tennis a rayuwarsa, bayan da ya sha kashi a hannun lamba daya na duniya Jannik Sinner a wasan karshe na Shanghai Masters ranar Lahadi. A bangaren mata kuma Aryna Sabalenka ta zamanto 'yar wasa ta farko da ta lashe gasar Wuhan ta China karo uku a jere, bayan casa Zheng Qinwen a wasan karshe ranar Lahadi.

'Yar kasar Kenya Ruth Chepngetich ta kafa sabon tarihi

A bangaren tseren famfalaki, 'yar kasar Kenya Ruth Chepngetich ta kafa wani sabon tarihi a gasar Chicago Marathon bayan nasarar lashe gasar a cikin sa'o'i 2 da mintuna 9, inda ta goge tarihin da 'yar Habasha Tigst Assefa ta kafa a baya.

Ana dab da soma cinikayyar 'yan wasan kwallon kafa a Turai

'Yan wasan Arsenal na fafatawa da takwarorinsu na Bayern MünchenHoto: Matthew Childs/Reuters

A cikin watan Janairun sabuwar shekara mai kamawa za a bude kasuwar cinikayyar 'yan wasan kwallon kafa a Turai, tuni jaridu da dama suka fara hasashen 'yan wasan da ka iya sauya sheka, ciki har da mai tsaron bayan Arsenal William Saliba, wanda Real Madrid ke fatan dauka. Manchester United ta tuntubi mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Stuttgart da ke nan Jamus Sebastian Hoeness, don maye gurbin Erik ten Hag da shi, a gefe guda kuma akwai yiwuwar ta tattauna da Thomas Tuchel, wanda kuma ake ganin yana iya karbar aikin horas da 'yan wasan kasar Ingila.