An shawo kan wutar daji a Portugal
July 27, 2017Talla
Wutar dajin wacce ta yi kwanaki biyar tana ci da karfin gaske a yankin tsakiya na kasar, a yanzu wani babban jami'in gwamnatin da ke kula da ayyukan jin kai ya ce karfin ta ya rage kishi 90 cikin dari. Musammun ma a agarin Serta da ke cikin jihar Castelo Branco inda aka baza 'yan kwana-kwana 1200 tun ranar Lahadin da ta wucce.