1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Shugaban kasar Koriya ta Kudu ya kafa dokar ta-baci

Suleiman Babayo ATB
December 3, 2024

Masu zanga-zanga sun mamaye majalisar dokokin Koriya ta Kudu bayan Shugaba Yoon Suk Yeol ya kafa dokar ta-baci. An shiga yanayin rudani bayan shugaban kasar ya kafa dokar ta-bacin.

Masu zanga-zanga sun mamaye majalisar dokokin Koriya ta Kudu bayan Shugaba Yoon Suk Yeol  ya kafa dokar ta-baci
Masu zanga-zanga sun mamaye majalisar dokokin Koriya ta Kudu bayan Shugaba Yoon Suk Yeol ya kafa dokar ta-baciHoto: Kim Soo-hyeon/REUTERS

Shugaba Yoon Suk Yeol na kasar Koriya ta Kudu ya kafa dokar ta-baci lokacin wani jawabi da ya gabatar kai tsaye ta kafofin yada labarai a wannan Talata. Shugaban ya zargi 'yan adawa da suka mamaye majalisar dokokin kasar yin sako-sako game da batun kasar Koriya ta Arewa duk da yadda take zama barazanar tsaro ga kasarsa.

Karin Bayani: Koriya ta Kudu: Jam'iyyar PPP da ke mulki ta rasa rinjaye

Shugaban ya ce ya kafa dokar ta-bacin domin domin magance 'yan kanzagin Koriya ta Arewa da tabbatar da kundin tsarin mulkin kasar game da 'yancin fadin albarkacin baki. Tuni jagoran 'yan adawa na kasar Lee Jae Myung ya matakin shugaban kasar a matsayin abin da ya saba kundin tsarin mulki. A daya bangararen majalisar dokokin kasar ta kada kuri'an watsi da matakin kafa dokar ta-bacin abin da ya jefa kasar ta Koriya ta Kudu cikin wani sabon rikicin siyasa.