An shiga zagaye na karshe na taron tantance makomar lardin Kosovo
March 10, 2007Manyan shugabannin Sabiya da na Albaniyawan Kosovo sun shiga zagaye na karshe na wata tattaunawar da suke yi a Vienna babban birnin Austria, akan wani shirin MDD da zai tantance makomar lardin Kosovo. Shugabannin kabilar Albaniyawan Kosovo sun albarkaci wannan shiri amma jami´an Sabiya sun yi watsi da shi suna masu korafin cewa ya tanadi bawa lardin na Kosovo ´yancin kai sannu a hankali. A bara aka fara shawarwarin akan makomar Kosovo amma gaba daya suka cije kuma ba´a tsammanin samun wani ci-gaba a taron na yau asabar. Shugaban Albaniyawan Kosovo Hashim Thaqi ya nuni da cewa.
“Mu dukkan mu a Kosovo muna aiki tukuru don yanke wata shawara mafi dacewa, shawara ta samun ´yanci. Masalaha a garemu, mu ´yan Kosovo ita ce girmama bukatar al´umar mu. Wato Kosovo ta zama kasa mai cikakken ´yanci.”
Bayan taron za´a mikawa kwamitin sulhu, shawarar da MDD ta bayar game da makomar lardin na Kosovo don ya albarkace shi.