An soke shari'ar da ake wa likitocin Maradona
May 29, 2025
A wani abu da ake ganin abin kunya ne ga tsarin shari'a a kasar Argentina, alkali Maximiliano Savarino ya ce halin da abokiyar aikin sa Julieta Makintach ta yi, ya haifar da nuna kyama ga shari'ar da aka fara a watan Maris kuma ta riga ta saurari shaidu sama da 40.
Wannan matakin na nufin za a gudanar da sabon shari'a tun daga farko, tare da kwamitin alkalai dabam-dabam. Makintach, daya daga cikin alkalai uku, ta janye daga shari'ar bayan da ta bayyana cewa an yi hira da da ita a wasu jerin shirye-shiryen talabijin game da shari'ar, abin da take gani mai yuwuwa ya karya wasu ka'idoji.
Bayan samamen da 'yan sanda suka kai tare da dakatar da shari'a na mako guda, an zargi Makintach mai shekaru 47 da keta mata hakkinta, da yin tasiri da kuma cin hanci da rashawa na kasancewarta a cikin gjeren zango na shirin talabijin mai taken "Divine Justice."
An yi gwanjon rigar Diego Maradona
Diego Maradona daya daga cikin manyan 'yan wasan kwallon kafa a duniya, ya mutu a watan Nuwamban 2020 yana da shekaru 60 a lokacin da yake murmurewa daga tiyatar kwakwalwa. An gano cewa ya mutu ne sakamakon gazawar zuciya da matsananciyar kumburin huhu.
Masu gabatar da kara, sun gurfanar da tawagar likitocinsa mutum bakwai a gaban kotu kan zargin sakacin kula da lafiyarsa a gida. Tawagar ta fuskanci hukuncin zaman gidan yari tsakanin shekaru takwas zuwa 25.