1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soke kakakin majalisar Ukraine

Abdul-raheem Hassan
October 7, 2021

'Yan majalisar dokoki a kasar Ukraine, sun kada kuri'ar korar kakakinsu Dmytro Razumkov saboda jayayya da shugaban kasa Volodymyr Zelensky.

Ukraine Parlamentspräsident Dmytro Rasumkow
Hoto: picture-alliance/Photoshot

Ana ganin fitaccen dan siyasar mai shekaru 38 a matsayin babban abokin hamayyan Shugaba Zelensky a zaben shugaban kasa na shekarar 2024.

Tsohon shugaban majalisar dokokin na Ukraine Razumkov, ya sha sukar manufofin shugaban kasar, ciki har da soke takunkumin gwamnati kan masu adawa da kafofin watsa labarai ba tare da hukuncin kotu ba.