An soki hukuncin da aka yanke wa masu fafatuka a Angola
March 30, 2016Ma'aikatan shari'a a kasar Angola sun yi tir da hukuncin da ake yanke wa wasu 'yan fafatuka 17 na wata kungiya da ake kira Luanda Book Club. Daukacin masu shari'a a kasar ta Angola sun yi amanna cewa ba a yi wa mutanen adalci ba, suna masu cewa hukuncin na da alaka da wani mulki na kama karya, kuma zai yi mummunan tabo ga tsarin shari'ar kasar. Francisco Viena mai shari'a ne a kasar ta Angola.
"A gani na wannan shari'a ba ta da wani hurumi a shari'ance. Ba a yi adalci ba. Kotuna ba za su iya yanke hukuncin da zai tauye 'yancin walwala ba. Wata kotu ta wata kasar mulkin kama karya ta yanke hukuncin."
A ranar Talata wata kotu a Angola ta yanke wa masu fafatukan 17 hukuncin daurin shekaru biyu zuwa takwas a gidan maza bayan ta same su da laifin kulla wata makarkashiyar hambarar da gwamnatin Angola. Tuni dai lauyoyinsu suka ce za su daukaka kara a kotun kolin kasar.