1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soki manufar ketare ta Syria

December 31, 2005

Tsohon mataimakin shugaban kasar Syria Abdel Halim Khaddam yayi murabus daga jam´iyar da ke mulki a kasar. Khaddam wanda ya dade akan mukamin, ya dauki wannan mataki ne jim kadan bayan ya soki lamirin manufar ketare ta Syria karkashin shugaba Bashar al-Assad, wadda ta janyo janyewar dakarun kasar daga Lebanon a cikin watan afrilu. Khaddam ya ce gwamnatin shugaba al-Assad ta tabka kurakurai da dama ciki har da na kokarin kare tsohon shugaban hukumar leken asirin ta a Lebanon Janar Rustom Gahzali. Khaddam ya ce Syria ta yi ta yiwa tsohon FM Lebanon Rafik Hariri barazana tun gabanin harin bam din da ya halaka shi a cikin watan fabrairu. Syria dai ta musanta hannu a kisan tsohon FM na Lebanon, duk da kashin kajin da wani binciken MDD akan kisan ya shafawa jami´an Syria.