An soki matakin kasar Brunei na tsaurara dokokin kasar
April 1, 2019Majalisar Dinkin Duniya ta yi suka da kakkausan lafazi kan matakan da kasar Brunei ke shirin dauka na tsananta dokokin hukunta masu aikata laifi a kasar.
Hukumar kula da hakkin dan Adam ta majalisar ta yi kira ga gwamnatin kasar ta Brunei da ta dakatar da mayar da sabbin matakan doka. Matakan sun tanadi hukuncin kisa ta hanyar jifa ga ma'aurata da aka same su da lafin yin zina da kuma 'yan luwadi. Da kuma yanke hannun wanda aka samu da laifin yin sata.
Mai magana da da yawun ofishin kula da hakkin dan Adam ta majalisar Dinkin Dunyia Ravina Shmadasani ta ce hukumar na kira ga gwamnatin Brunei da ta dakatar da kafa wannan doka da take shirin yi a ranar Laraba. Ta ce idan aka aiwatar da dokar, hakan zai zama koma baya ga 'yancin al'umar kasar Brunei, inda kashi biyu bisa uku Musulmi ne, ragowar kuma Kirista ne da 'yan addinin Bhudda da su ma dokar za ta yi aiki kansu.
Ko da yake kasar na da tsauraran dokoki amma tun a 1957 ba ta aiwatar da hukuncin kisa ba.