1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soma rigakafin Covid-19 a Najeriya

Uwais Abubakar Idris
March 5, 2021

Najeriya ta kaddamar da shirin rigakafin allurar Covid-19 inda aka soma da ma'aikatan kiwon lafiya a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar da ta yi mumunan illa ga rayukan jama'a.

Nigeria Covid-19 Impfung in Abuja | Dr. Cyprian Ngong
Wani jami'in kiwon lafiya na karbar allurar rigakafin coronaHoto: Uwais Idriss/DW

Kaddamar da alluran rigakafin karkashin hukumar kula da lafiya matakin farko ta Najeriya, ya kawo karshen dogon jiran da aka dade ana yi na dakon alluran da ma yadda za a aiwatar da aikin ga jama'a.

Shekaru biyu za a shafe a na yi wa jama'a daga ko ina cikin kasar Najeriya masu shekaru kama daga 18 zuwa sama alluran rigakafin, a cewar babban sakataren ma'aikatar lafiya a Najeriya Dr Abdulazi Mashi. 

Jami'an kiwon lafiya hudu ne aka fara yi wa allurar rigakafin a gaban jama'a a, yayin kaddamar da bikin a Abuja, kana wadanda aka yi wa rigakafin dukkaninsu sun dade suna aikin kula da wadanda suka kamu da cutar ta Covid 19 ciki har da Farfesa Yunusa Attahiru da ya bayyana jin dadinsa da matakin allurar.

Hoton barkwancin Corona

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a Najeriyar ta gamsu da yadda aka soma alluran, kuma wakilinta Dr Walter Kazadi Mulombo ya bayyana muhimmancin fara yi wa ‘yan Najeriya rigakafin cutar ta covid 19 inda ya ce "Muna alfahari da ganin wannan al'amari mai tarihi, kuma wannan allura za ta taimaka mana wajen hanzarin shawo kan cutar nan, dole mu ci gaba da daukan matakan kare kai na kula da lafiya.'' Har yanzu akwai ‘yan Najeriyar da suke nuna dari dari da kin yarda da allurar rigakafin, an kuma tsara yi wa shugaban kasar da mataimakinsa da sauran manyan jami'an gwamnatin Najeriya da shuwagabanin Addinai rigakafin domin kawar da duk wani shakku na wata illa ga maganin. Babu tillas a kan kowa sai dai kwarin guiwa na ganin kowa ya tabbatar da an yi masa allurar ta hanyar yin rijista a shafin yanar guzo da aka samar.