1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soma ganin alamun sasanta Hamas da Isra'ila

October 8, 2025

Bangarorin Isra'ila da Hamas sun nuna kyakkyawar alamu na cimma yarjejeniya domin kawo karshen yakin shekaru biyu, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban Falasdinawa tare da lalata galibin sassan yankin Gaza.

Masar, inda ake tTattaunawar neman zaman lafiya tsakanin Hamas da Isra’ila
Hoto: Khaled Desouki/AFP/Getty Images

Rahotanni daga kasar Masar na cewa akwai alamun samun ci gaba mai kyau a tattaunawar kai tsaye ta hannun masu shiga tsakanin Isra'ila da Hamas, kamar yadda shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi ya bayyana.

A yau Laraba, jakadu daga Amurka sun shiga cikin tattaunawar da ke gudana a kan shirin samar da zaman lafiya da Amurka ta gabatar.

Haka kuma, Firaministan Qatar da shugaban hukumar leken asirin Turkiyya sun isa birnin Sharm el-Sheikh, inda ake ci gaba da tattaunawar tun a ranar Litinin.

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, ya bayyana cewa shugaban Amurka Donald Trump ne ya roki gwamnatin Ankara da ta taimaka wajen shawo kan Hamas domin cimma yarjejeniya.