Kungiyar AU ta kasashen Afirka na taronta karo na 37
February 15, 2024Talla
Tun farko a ranar Larabar majalisar zartaswar ta kungiyar da ta kunshi ministocin harkokin waje ta bude taron share fage. Sabbin juyin mulki da aka yi Nijar da Gabon da, rikicin siyasar Senegal, da Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango da sauran wasu batutuwan taron zai fi mayar da hankali a kansu da kuma shirin shigar kungiyar a cikin kungiyar G20 a cikin watan Satumbar da ke tafe.Kasashen Nijar da Gabon ba za su kasance ba a taronba, bayan kungiyar ta dakatar da su saboda juyin mulkin da aka yi a cikin kasashen biyu