NATO za ta maye gurbin jiragen leƙen asiri na AWACS
July 7, 2026
Talla
Shugaban rundunar tsaro ta NATO Mark Rutte ya sanar da kwangilolin makamai da dama, ciki har da daya daga kamfanin Airbus na Turai, a rana ta farko na taron kungiyar da ake yi a Ankara, a Turkiyya.
A ƙarshen shekarar ta 2023 NATO ta yi furcin cewar tana da niyyar maye gurbin jiragen leƙen asiri na AWACS, waɗanda kamfanin Boeing na Amurka ke ƙerawa da take yin amfani da su.
Yanzu haka shugaban Amurka Donald Trump ya isa a birnin Ankara na Turkiyyar a yau domin halarta taron na NATO.