1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An soma taron kolin kasashen G20 a Italiya

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
October 30, 2021

Kasashen duniya mafi karfin tattalin arziki da masana'antu na taron kolinsu a birnin Roma na kasar Italiya da nufin duba batutuwan da suka addabi tattalin arzikin duniya da sauyin yanayi.

Italien Rom | G20 Gipfel
Hoto: Pavel Bednyakov/SNA/imago images

Shugabannin gwamnatoci da na kasashen G20 sun soma taron kolinsu na kwanaki biyu a birnin Roma na Italiya a wannan Asabar, da zummar duba batutuwan da suka fi daukar hankalin kasashen mafi karfin tattalin arziki na duniya. Batun gibin da annobar corona ta haifar a fannoni da dama musamman na tattalin arziki na daga cikin batutuwan da shugabannin za su mayar da hankali a taron:

A yayin da yake jawabin bude taron mai masaukin baki firaministan Italiya Mario Draghi , cewa yayi kama daga batun annobar corona izuwa ga batun sauyin yanayi da tsarin haraji na bai daya mafi ingnaci, ba wani zabi ba ne wani yace zai yi gaban kansa, saboda hakan yana da kyau mu hada karfi da karfe dan tunkara da warware wadannan matsaloli tare.

Sai dai taron na gudana ne ba tare da halartar shugabannin Rasha da Chaina ba kai tsaye illa ta hanyar bidiyo, lamarin da masu sharhi ke cewa rashin kasancewarsu a taron na birnin Roma, ka iya haddasa nakasu kan wasu muhimman batutuwan da kasashen ka iya cimma.