1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

An tabbatar da mutuwar matar marigayi jagoran addinin Iran

March 2, 2026

An tabbatar da mutuwar matar marigayi Ali Khamenei na Iran, Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh sakamakon raunukan da ta samu a harin Amurka da Isra'ila

Birnin Tehran na Iran
Birnin Tehran na IranHoto: Fatemeh Bahrami/Anadolu/picture alliance

Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu babu dakarun Amurka a cikin Iran, amma ya jaddada cewa Washington za ta dauki duk matakin da ya dace a Tehran.

Birnin Tehran na IranHoto: Fatemeh Bahrami/Anadolu Agency/IMAGO

A halin da ake ciki yanzu birnin Tehran ya zama tamkar kufai, inda aka ga jama'a da dama na barin gidajensu dauke da jakunkuna. A kasuwar Tajrish, mutane sun rika sayen abinci cikin gaggawa, yayin da warin konewa ke tashi kusa da hedikwatar talabijin na gwamnati da aka kai wa hari.

Wasu mazauna birnin sun bayyana tsoro da fargaba duk lokacin da suka ji karar fashewar bam, yayin da wasu ke cewa duk da tsoron, suna kuma fatan rikicin zai kawo karshen gwamnati