1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tabbatar da mutuwar mutane 93,000 a rikicin Siriya

June 13, 2013

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin dan Adam ta tabbatar da mutuwan mutane 93,000 cikin rikicin Siriya.

Iraqi and Syrian Kurdish refugees cross the Iraqi-Syrian border illegally near Faysh Khabur, Iraq, on Tuesday, August 14, 2012. David Enders/MCT /LANDOV AOL, GOOGLE, YAHOO OUT. Rechtevermerk
Hoto: picture-alliance/dpa/landov

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ke kare hakkin dan Adam ta tabbatar da mutuwan mutane 93,000 cikin rikicin da ke ci gaba da ritsawa da kasar Siriya, kuma ta ce, akwai yuwuwar adadin ya haura haka.

Ofishin hukumar ya ce, an tattara alkaluman daga watan Maris na shekara ta 2011 zuwa watan Afrilu na wannan shekara ta 2013.

Shugabar hukumar Navy Pillay ta ce, akwai matukar wuya a tantance hakikanin mutanen da suka mutu tun lokacin da aka kaddamar da boren neman kawar da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta kasar ta Siriya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halama Balaraba Abbas