An kawo karshen yaki a Habasha
December 12, 2022Kawo yanzu an tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu, abin da ke nuna alamun kawo karshen yakin basasan na shekaru biyu da ya janyo salwantar rayuka da dama. Masu sharhi kan harkokin yau da kullum na ganin tsagaita wutar na da tasiri kan samun zaman lafiya musamman a yankunan da aka samu tashe-tashen hankula na Tigray da Amhara gami da Afar. Dr. Taye Negussie mai binciken harkokin siyasa a jami'ar birnin Addis Ababa ya ce duk bangarorin sai sun ci gaba da nuna sanin yakamata: "Harkokin rayuwa da na kasuwanci da ake yi a baya ake bukatar mayar da su. Ba za manta da abin da ya faru ba, za a koyi yafewa domin rayuwa tare. Yana da kyau sasantawa ta siyasa a matakin kasa, kamar yadda ake maganar yafewa juna. Ba za a iya mantawa da abin da ya faru ba, amma za a ci gaba da rayuwa da mu'ammala kan harkokin rayuwa da kasuwanci. Akwai abubuwan da za su iya zagon kasa kan tattaunawar zaman lafiya. A hannu daya akwai kasashe ketere da kafofin sada zumunta kana babu wani binciken da aka yi na sanin wadanda suka aikata ta'asa daga duk bangarorin.
Gwamnatin Habasha na neman taimakon jama'a domin kara samar da zaman lafiya
Firaminista Abiy Ahmed na kasar ta Habasha ya bukaci masana su taimaka wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa. Ita kanta hukumar sasantawa ta kasar ta ce tuni shiri ya yi nisa kan tabbatar da ganin an dinke barakar da aka samu sakamakon yakin basasan. Dr. Yonas Adaye ke zama hukumar tattaunawa ta kasar: "Ina tsammanin akwai lokaci da yanayin yaki kana kawai lokaci da yanayin zaman lafiya kamar yadda masu iya magana cewa. Yanzu lokaci ne na zaman lafiya, muna aiki kan tabbatar da taswirar zaman lafiya. Duk za mu je ganawa da mutanen yankin Tigray. Muna kuma ganin irin ci-gaban da ake samu. Idan wannan ci-gaban ya karfafa za mu samu damar ida garin Mekelle lokacin."
Martanin jama'ar kasar a game da shirin zaman lafiyar
Ga sauran 'yan kasar Habasha abin da suke bukata shi ne zaman lafiya kamar yadda Adene Berhanu mazauniyar birnin Addis Ababa da ke cewa lokaci ya yi na samun zaman lafiya: "Lokaci ne na samun sabon gwarzo mu dade muna samun wadanda ake girmamawa saboda yaki. Muna son sabon gwarzo wanda yake imani da tattaunawa. Duk bangarorin ya dace su hau teburin tattaunawa. Mata da yara rikicin ya fi shafa, lokacin ya yi na kawo karshen haka. Mun yi imanin a karni na 21 komai za a iya tattaunawa a kai." Mutane da dama sun yi maraba da shirin zaman lafiya tsakanin gwamnatin kasra ta Habasha da mayakan yankin Tigray, abin da suke gani zai iya kawo karshen takun saka tsakanin bangarorin biyU.