An tarwatsa gangami masu zanga-zanga a Nairobi
May 9, 2016'Yan sanda a kasar Kenya sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa magoya bayan 'yan adawa da shugabanninsu da ke zanga-zanga a wajen ofisoshin hukumar zaben kasar da ke birnin Nairobi. Jagororin 'yan adawa na saka ayar tambaya game da hukumar zaben a matsayin 'yar baruwanta sannan sun nuna bukatar a rushe ta gabanin zaben shekarar 2017. Farfesa Anyang Nyong jagoran 'yan adawa ya ce wasu ke juya akalar hukumar zaben.
"Hukumar zabe ba ta da sauran mutunci, ta aikata ba daidai ba a zaben da ya gabata, ba ta kuma nuna alamar canji ba, saboda haka ba za mu yarda a shirya zabe na gaba da yadda hukumar take a yanzu ba. Ba ma son mu jefa kasar nan cikin matsaloli, saboda haka muke kira da a samar da hukumar zaben da za ta yi aiki da gaskiya da rikon amana."
Kenya dai ta yi fama da mummunan rikicin bayan zaben 2007 da ya yi sanadin rayukan mutane fiye da dubu daya sannan dubun dubata suka rasa matsugunansu.