An tarwatsa masu zanga-zanga a Myanmar
February 9, 2021Talla
Masu zanga-zangar dai na son dawo da mulkin farar hula a kasar da ma neman sakin shugabar kasar Aung San Suu Kyi da ke tsare tare da wasu mukarabban gwamnatinta.
Tun a daren jiya ne dai shugabanin sojin da ke jagorantar kasar a yanzu suka bada sanarwar sanya dokar hana taruwar mutum fiye da 5 da kuma takaita zirga-zirga daga karfe 4 na safe zuwa 8 na dare a babban birnin kasar biyo bayan zanga-zangar da dubban mutane ke yi tun a ranar Asabar din da ta gabata.
Rahotanni na nuna cewa a wannan Talatar jami'an tsaro sun kama mutum a kalla 27 a birnin Mandalay na kasar.