1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tashi dutse hannun riga a taron koli na birnin Munich

Ahmed Salisu
February 18, 2019

Taron koli kan tsaro a duniya da aka kammala birnin Munich na Jamus ya tashi da takaddama tsakanin Angela Merkel ta Jamus da mataimakin shugaban Amirka.

Deutschland Münchner Sicherheitskonferenz
Hoto: Imago/S. Zeitz

Batun makamashi da hada karfi da karfe waje guda yayin tinkarar lamura a duniya da ma yarjejeniyar nan ta Nukiliyar Iran na daga cikin abubuwan da suka haifar da wannan ja-in-ja wanda tuni ya fara haifar da maida martani iri-iri.

Yayin gabatar da jawabinta a wajen taron na Munich wanda jama'a da dama suka jinjinawa, Angela Merkel ta bukaci kasashen duniya da su hada karfi waje guda don tinkarar al'amuran da yanzu haka kasashen duniya ke fuskanta muamman wanda suka danganci harkoki na tsaro. Wani abu har wa yau da shugabar gwamnatin ta Jamus ta mayar da hankalinta a kai shi ne cigaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran wadda Amirka ke adawa da shi.

Mataimakin shugaban Amirka, Mike PenceHoto: Reuters/M. Dalder

Wannan ne ma ya harzuka mukaddashin shugaban Amirka Mike Pence a lokacin da ya gabatar da nasa jawabi a wajen taro, inda ya ke cewar lokaci ya yi da kasashen duniya za su dakatar da yi wa yunkurin kasar na daukar matakai kan wasu kasashe kafar ungulu.

 

''Lokaci ya yi da dukanninmu za mu yi aiki tare wajen dakatar da Turai kan yadda ta ke yi wa yunkurin Amirka zango kasa musamman ma kan takunkumin da muka kakabawa Iran. Lokaci ya yi da Turai za ta hada kai da mu kana ta juyawa Iran da kawayenta baya. Lokaci ya yi da Turai za ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran sannan ta hada hannu tare da mu wajen matsawa kasar lamba ta fuskar tattalin arziki da diflomasiyya don baiwa al'ummar kasar da na yankin tsaro da 'yancin da suke bukata''

Baya ga batun na Iran, wani lamari da ya da ya haifar da takun saka tsakanin Merkel da ence shi ne batu na makamashi musamman ma dai maganar nan ta shimfida bututun iskar gas daga Rasha zuwa Jamus wanda zai bai ta yankin Baltic, batun da Amirka ke ganin mayar da hankalin kan Rasha ta fuskar samun iskar Gas kamar wani yunkuri ne na juya mata ba sai dai Merkel ta ce ba haka lamarin yake ba.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela MerkelHoto: Reuters/A. Gebert

''Babu wanda zai iya cikakken bayani game da dogaron kasarmu kan Rasha don samun iskar Gas idan har aka mayar da hankali kan irin buun da aka yi amfani da shi wajen tura iskar gas din. A shirye nake kuma kuma ya kamata a sani ba wanda ke son dogaro kacokan kan Rasha''

 

Tuni dai mutane da dama suka fara mayar da martani kan wannan takaddama ta shugabannin biyu. Daga cikin wanda suka yi martani kan kalaman na Pence har da tsohon mataimakin John Kerry wanda ke cewar kalaman na Pence abin kunya ne ga Amirka inda ya kara cewar kyautuwa ya yi ataimakin shugaban ya fi mayar da habkali kan batun da ya danganci sauyin yanayi da e addabar duniya maimakon mayar da hankalinsa kan batun yarjejeniyar Iran.