An tsagaita wuta a Sudan ta Kudu
May 11, 2014Talla
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce an fara aiki da yarjejeyar tsagaita wuta wadda ta kawo karshen yakin basasan kasar na watanni biyar.
Ranar Jumma'a Shugaba Salva Kiir da madugun 'yan tawaye kuma tsohon mataimakin Shugaban kasa Riek Machar suka rantaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, yadda ta tanadi tsagaita wuta cikin sa'o'i 24. Kasashen duniya da suka saka kaimi wa bangarorin sun yi maraba da yarjejeyar.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu