An tsare mutane 82 a Turkiyya
November 10, 2017Dubun wadannan mutane ya cika ne bayan da 'yan sanda suka kaddamar da somname kan wasu cibiyoyi 14 da aka samu labarin suna nika garin zuwa Siriya. Wata kafar yada labaran kasar Turkiyya ta ruwaito cewa an taba samun wadan da aka tsaren da zargin alaka da kungiyar I S bayan kama wasu 'yan Siriya 11 a Kudancin kasar.
Kame mutane 82 da shirin shiga Siriya na zuwa ne kwana guda bayan bayan da 'yan sanda 1,500 suka kaddamar da somame kan gungun 'yan ta'addan I S 245 a birnin Ankara, tare da garkame mutane 173 da ake tuhuma da laifukan ta'addanci.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Turkiyya ta ce jimillan 'yan ta'adda 450 ne ke tsare, bisa zargin tallfawa mayakan masu tsauraran akidu. Sama da shekaru biyu kenan Turkiyya ke fuskantar hare-hare da ake daura alhakki kungiyar I S ciki har da harin wani dan bindiga da ya kashe mutane 39 bayan bude wuta a babban gidan rawan Instanbul.