An tsare ´yan adawa da dama a Pakistan
September 23, 2007Talla
Makonni biyu gabanin zaben shugaban kasa da za´a gudanar a Pakistan inda bisa ga dukkan alamu za´a sake zaben shugaba Pervez Musharraf, ´yan sanda sun tsare shugabannin adawa da dama. An dai dauki wannan mataki ne musamman akan ´ya´yan jam´iyar Muslim Lig ta tsohon FM Nawaz Sharif da kuma wani kawancen jam´iyun Islama. Da farko ´yan adawa sun lashi takobin hana majalisar dokoki sake zaban Musharraf a ranar 6 ga watan oktoba. An kame su ne a wani samame da jami´an tsaro suka kai a Islamabad babban birnin kasar. ´Yan adawa sun yi tur da kamen da cewa haramun ne kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa. To sai dai ´yan sanda sun ce sun dauki matakin ne don rigakafi tare da tabbatar da tsaro da bin doka da oda.