1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsaurara matakan tsaro a birnin London bayan kisan wani soja

May 23, 2013

A ranar Laraba wasu matasa biyu suka kashe wani mutum da gwamnati ta ce sojan Birtaniya ne, a bayyanar jama'a.

AATTENTION EDITORS - VISUAL COVERAGE OF SCENES OF INJURY OR DEATH A man with bloodied hands and knives walks across a street past the body of a man in a still image from amateur video that shows the immediate aftermath of an attack in which a man was killed in southeast London May 22, 2013. A man was hacked to death in a street near an army barracks in London on Wednesday in what Prime Minister David Cameron said appeared to be a politically motivated attack. MANDATORY CREDIT to ITV News. REUTERS/ITV News via Reuters TV (BRITAIN - Tags: CRIME LAW MILITARY CIVIL UNREST) USE FOR 48 HOURS ONLY. NO SALES. NO ARCHIVES. FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. NO ONLINE USE. NOT FOR SALE FOR INTERNET DISPLAY. MANDATORY CREDIT. TEMPLATE OUT
Hoto: Reuters

'Yan sanda a birnin London sun tsaurara matakan tsaro a kewayen barikokin Birtaniya bayan wani hari da aka kai a birnin ranar Laraba da yamma, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum guda. Gwamnatin kasar ta bayyana harin da cewa na ta'addanci ne. A ranar Laraba wasu matasa biyu bakar fata dauke da makamai suka kashe wani mutum da gwamnati ta ce sojan Birtaniya ne, a bayyanar jama'a a unguwar Woolwich dake kudu maso gabacin babban birnin na Birtaniyya. A dangane da wannan harin Firaministan Birtaniya David Cameron ya katse wata ziyarar da yake yi a Faransa, ya koma gida inda ya jagoranci wani taron gaggawa na kwamitin harkokin tsaron kasa, inda ya bayyana cewa.

"Da farko wannan kasa za ta dage a kan matsayinta na yaki da tsattsauran ra'ayi da kuma ta'addanci. Ba za mu mika wuya ga kowane irin nau'i na ta'addanci ba. Na biyu dukkan al'umar wannan kasa na da wannan ra'ayi, wannan hari ne a kan Birtaniya da salon rayuwarta, kuma hari ne na bijire wa Musulunci da al'ummar Musulmi dake ba da gagarumar gudunmawa don ci-gaban wannan kasa."

Wannan lamarin ya auku ne kwanaki uku gabanin wasan karshe na cin kofin zakarun kwallon kafar Turai na Champions League a London, inda za a kara tsakanin kulob din Jamusawa guda biyu.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu