An tsaurara tsaro a Indiya
April 10, 2019Talla
Hukumomi a kasar sun baza dubban jami'an sanda da sauran wasu masu kayan sarki a sassan jihohi 29 da wasu cibiyoyi biyu na tarayya, gabanin zaben 'yan majalisar dokoki.
A mazabu 91 ne za a fara zaben a tashin farko a ranar Alhamis, zaben kuma da za a yi a matakai bakwai daban-daban, a kuma kammala ranar 19 ga watan gobe na Mayu.
An dai tsananta matakan tsaro a yankunan Jammu da kuma jihar Kashmir, wadanda duk ke fama da fitintinu.
Akwai wasu rahotanni da ke cewa dakaru za su yi sintiri na musamman, a dukkanin wuraren da ke kan hadarin fuskantar barazana lokacin zaben.