An tsige mataimakiyar shugaban Philippines Sara Duterte
May 11, 2026
Majalisar wakilai ta kasar Philippines ta tsige mataimakiyar shugaban kasa Sara Duterte a yau Litinin, sakamakon samunta da laifin tara dukiya da ba a san tushenta ba, da kuma barazanar kisa da ta yi wa shugaban kasa Ferdinand Marcos Jr.
Kudurin tsige matamaikiyar shugaban kasar ya samu kuri'u 257, yayin da 25 suka hau kujerar na ki, sai guda tara da ba su halarci zaman majalisar ba.
Karin bayani: Za a fara shari'ar tsohon shugaban Philippines a kotun ICC
Abin da ya rage yanzu shi ne mika batun gaban majalisar dattijai, domin tuhumarta da wadannan zarge-zarge biyu, wadanda ke zama tarnaki ga kudurinta na neman takarar shugabancin kasar a shekarar 2028.
Karin bayani: Kusan mutum 100 sun mutu sakamakon guguwa a Philippines
Shi ma tsohon shugaban kasar ta Philippines Rodrigo Duterte, wanda shi ne mahaifin mataimakiyar shugaban kasa da majalisa ta tsige Sara Duterte, na fuskantar tuhumar kisan dubban jama'a, lokacin da yake rike da kujerar magajin birnin Davao, da kuma lokacin da yake shugabancin kasar.
Karin bayani:Tsohon shugaban Philippines na fatan tsallake shari'ar ICC
Haka zalika shi ma tsohon shugaban 'yan sandan kasar Roland dela Rosa, na fuskantar makamanciyar wannan tuhuma ta kashe dubban fararen hula a karaskhin mulkin Mr Duterte.