An tsige shugaban majalisar Brazil
September 13, 2016A Brazil majalisar dokokin kasar ta tsige shugabanta Eduardo Cunha daga mukaminsa na dan majalisa bayan da kwamitin bincike kan badakalar kudin kamfanin man fetur na Petrobas da majalisar ta girka ya bankado sirrin shugaban majalisar na mallakar wani asusun ajiyar kudi nasa na asirce a wani banki a kasashen ketare.
'Yan majalisar dokokin kasar ta Brazil sun dauki wannan mataki a cikin wata sanarwa da suka fitar a karshen wata zazzafar muhawara da suka shirya kan batun a zauran majalisar. Beto Mansur mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar ta Brazil shi ne ya karanto sanarwar:
Ya ce "Na bayyana faduwar kujerar dan majalisa Eduardo Cunha a bisa samun shi da aikata laifin da bai dace ba da mukamin dan majalisa"
Shi dai Eduardo Cunha ya kasance a sahun gaba na 'yan majalisar dokokin kasar ta Brazil da suka yi ruwa da tsaki wajen tsige shugabar kasar Dilma Rousseff daga kan mukaminta na shugabancin kasa yau da 'yan kwanaki. Sa idai har ya zuwa lokacin da ak tsige shi Shugaban majalisar dokokin kasar ta Brazil ya ci gaba da musanta zargin mallakar wani asusun ajiyar kudi banki na asirce a kasashen ketare yana mai cewa zargi ne da ba shi da tushe.