An tuhumi wani jigo cikin 'yan adawar kasar Kenya
February 6, 2018Talla
Jami'an 'yan sanda sun gabatar da takardar sammaci da ga wata kotun yanki da ke Kajiado a kasar ta kenya, inda ake tuhumar Miguna Miguna da shiga gaba lokacin wani gangami ba bisa ka'ida ba tare da cin amanar kasa ta hanyar rantsar da Raila Odinga domin kama aiki a matsayin sabon shugaban mutanen kasar Kenya.
Zuwa yanzu dai gidajen talabijin masu zaman kansu a kasar sun sanar da cewar Miguna ya ki amsa laufukan da aka tuhume shi da su, jami'an tsaro sun kame shi a ranar Juma'a da ta gabata yayin da suka kai wani samame gidansa an kuma bayar da belinsa a kan kudi shilling dubu hamsin na kasar Kenya duk kuwa da cewar har yanzu yana hannun 'yan sanda.