An wanke wadanda ake zargi a hatsarin Saudiyya
October 1, 2017Talla
Kotun ta kuma wanke kamfanin Binladen da ke da alhakkin tsarin ginin masallacin daga tushe, kotun dai ta ce hukuncin ya wanke mjtanen ne sakamakon rashin gabatar da kwararan hujjuji aka laifin da ake thumar su da aikatawa. To sai dai kotun ta ce akwai damar daukaka wannan kara.
A tun farko dai an zargi mutanen ne da yin sakaci da kuma ka'idojin kula da lafiyar al'umma, amma a baya kotun ta ce ba ta da hurumin zartar da hukunci a kan laifin da ake tuhumar mutanen sanadiyar faduwar kugiya a kan masallata a cikin masallacin birnin Makka.