1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Makuden kudin rikcin zaben Najeriya na 2027

April 7, 2026

A wani abin da ke zaman alamun rikicin da ake shirin gani cikin fage na siyasar Najeriya a zabukan kasar na shekarar badi, gwamnatin kasar ta shirya kashe Naira miliyan dubu 135 domin shari'un zabe na kasar.

Zaben Najeriya
Zaben NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Ya zuwa yanzun dai Naira kusan Tiriliyan daya ne dai aka tsara hukumar zaben tarayyar Najeriya take shirin ta kashe a kokarin tabbatar da sahihan zabe cikin kasar a shekarar badi. Kafin wani sabon kasafin Naira miliyan dubu 135 da gwamnatin kasar tace ana shirin a batar domin shari'un zaben na shekarar badi.

Dalilin samar da kudin

Zaben NajeriyaHoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture alliance

Sabon adadin da ke zaman irinsa mafi girma a cikin tarihin zabe dai na kuma nuna alamun rigingimun da zabulan kasar na shekarar badin ke shirin fuskanta. Can cikin gidan tarihi dai dama ba kasafai zabukan kasar kan kare a runfunan yin zaben ba.

Magudi cikin fage na siyasa, ko kuma neman adalci a zaurukan alkalai, adadin dak e zaman irinsa mafi yawa a tarihin zabukan kasar dai, tuni ya fara dauka ta hankali cikin fagen siyasa. Naira miliyan dubu uku ne dai alal ga misali hukumar zaben kasar ta kai ga kare zabukan na shekara ta 2023 cikin gidan alkalan.

Kafin adadin da ke barazanar raba kai har a tsakanin lauyoyin dake taka rawa cikin shari'u na zabukan kasar.

Bangaren adawa

Zaben NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Kanwa uwar gami na zabuka, ko kuma reshe a bangare na masu mulki na kasar dai, tuni masu adawa ke zargin INEC din da so na zuciya a kokari na shirya zabukan dake da tasiri ga makomar demokaradiyyar Najeriya.

Zargin kuma da daga dukka na alamu ke iya rikida ya zuwa rigingimun dake iya kaiwa zuwa cikin gidan alkalan.

Barrister Saidu Mohammed dai wani lauya ne da ke shariu'un zabe a kasar, da kuma yake fadin kai na mage ya riga ya waye.

Miliyoyi cikin kasra a halin ynazu dai na zaman jiran tasirin alkalan a koakri na kwantar da zuciyar mai tsumma cikin fagen na siyasa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani