Taron COP31 ya kammala ba tare da cimma matsaya ba
November 23, 2026
Taron sauyin yanayi na duniya COP31 ya kammala a birnin Antalya na kasar Turkiyya a jiya Lahadi, ba tare da cimma matsaya ba, bayan da mahalarta taron suka gaza daidaitawa kan batun amfani da makamashin da ke gurbata muhalli.
Rashin daidaiton ya taso ne daga batun makamashi mai fitar da hayaki, musamman man fetur da iskar gas, inda kasashen Tarayyar Turai da wasu kasashe suka yi watsi da daftarin sanarwar karshe saboda rashin bayyana matakai masu karfi na rage amfani da irin wannan makamashi.
Sai dai wasu kasashe da suka yi fice wajen samar da mai kamar Saudiyyya da Rasha sun yi tsantsar adawa da irin wadannan ka'idoji, yayin da wasu kananan kasashe musamman na yankin Tekun Pasific suka nuna damuwa kan jinkirin daukar matakai da ke kara jefa su cikin hadarin tasirin sauyin yanayi.
Karin bayani: Taron sauyin yanayi na COP31 a Turkiyya ya gaza cimma wa'adinsa
Haka kuma taron ya tattauna batutuwan kudaden tallafi ga kasashe masu tasowa da hanyoyin kara amfani da makamashi mai tsafta, sai dai ba a cimma cikakkiyar yarjejeniya kan wadannan batutuwa ba.
Sakataren kula da sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya, Simon Stiell, ya bayyana takaicinsa kan gazawar taron, yana mai cewa duniya ba za ta iya ci gaba da fuskantar irin wannan koma baya ba, yayin da illolin sauyin yanayi ke kara kamari.
Karin bayani: Masana sun ce duniya na kara kusantar yanayin matsanancin zafi
Haka kuma, masu rajin kare muhalli sun nuna takaicinsu kan sakamakon taron, suna masu cewa gaza cimma yarjejeniya a taron COP31, na iya kawo cikas ga kokarin rage matsalar dumamar yanayi da ke ci gaba da haddasa ambaliyar ruwa da fari da matsanancin zafi a sassa daban-daban na duniya.