1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yaba wa hukunci ICC kan Ratko Mladic

Gazali Abdou Tasawa
November 23, 2017

Kungiyoyi da kasashen duniya sun bayyana gamsuwarsu kan hukuncin da kotun ICC ta yanke wa Ratko Mladic tsohon shugaban rundunar Sabiya a Bosniya jagoran kisan kiyashin da sojojin suka aikata a tsohuwar kasar Yugoslaviya.

Niederlande Urteil Ratko Mladic | Fernsehübertragung
Hoto: picture-alliance/AA/n: Ibrahimkadic

 

Da yake tsokaci kan wanann hukunci wanda kotun ta yanke a jiya Laraba, babban kwamishinan kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad al Hussein wanda ya bayyana Ratko Mladic a matsayin tushen zalunci, ya ce wannan hukunci na a matsayin wani kashedi ne ga duk wasu azzaluman duniya:

"Wannan hukunci wani hannunka mai sanda ne ga duk wasu masu aikata laifukan yaki na su fahimci cewa duk irin karfin ikon da suke takama da shi ko badan-badade za su kare a hannun shari'a."

Kungiyar Tarayyar Turai da ma kasar Amirka sun yi kira ga kasashe da al'ummomin yankin balkan da su yi aiki kafada da kafada domin gina makomarsu a tare.

Kotu dai ta samu Ratko Mladic dan shekaru 74 a duniya da aikata laifuka guda 10 da suka hada da kisan kiyashin da aka aikata a Srebrenica na tsohuwar kasar Yugoslaviya, inda sojoji suka hallaka Musulmi dubu takwas a shekara ta 1995.