An yake wa dakarun Sudan hukuncin kisa
December 30, 2019Wata kotu a kasar Sudan ta yanke wa wasu jami'an leken asiri 27 hukuncin kisa bayan da aka same su da laifin azabtarwa da ya kai ga mutuwar wani mai zanga-zangar nemen sauyi a watan Disamban bara. Cikin hukunci da ya yanke, alkali Sadok Abdelrahman ya nemi a rataye wadanda suka yi sanadin mutuwar malamin makaranta Ahmed al-Kheir Awadh bayan kama shi a jihar Kassala da ke gabashin kasar.
Idan za a iya tunawa a ranar 19 ga Disamban 2018 ne daruruwan ‘yan kasar ta Sudan suka fara zanga-zanga bayan da gwamnati ta ninka farashin biredi a daidai lokacin da ake tsaka da fama da komabayar tattalin arziki. Wannan zanga-zangar ta rikide zuwa boren wanda yayi awon gaba da kujerar mulkjin Shugaba Omar el-Beshir bayan shekaru 30 na mulki.
A cewar kungiyar Amnesty International, akalla mutane 177 sun mutu a lokacin da sojoji suka yi amfani da karfi wajen murkushe boren a ranar 3 ga watan Yuni a birnin Khartoum.